DolRise

FALALAN SALATIN ANNA I(S A W) *YININ JUMA’A, MAFI ALKHAIRIN YINI* 🕋 Mu yawaita yin salati ga Manzon Allah ﷺ a cikin wannan yini mai albarka na Juma’a, domin Juma’a rana ce mai falala da matsayi na musamman a Musulunci. 📖 Manzon Allah ﷺ ya ce: Mafi alherin yini da rana ta fito a cikinsa shi ne ranar Juma’a. A cikinta aka halicci Annabi Adam, a cikinta aka shigar da shi Aljanna, kuma a cikinta aka fitar da shi daga cikinta. Kuma Alƙiyama ba za ta tsaya ba face a ranar Juma’a.” 📚 Sahih Muslim, Hadisi na 854. 🤲 YA ALLAH! Ka sanya mu cikin bayinka masu yawan salati ga Annabinka Muhammad ﷺ, Ka karɓi ibadunmu, Ka gafarta mana zunubanmu, Ka kuma sanya mu cikin waɗanda za su rabauta a duniya da Lahira. اللَّهُمَّ صَلِّ وَسَلِّمْ عَلَى نَبِيِّنَا مُحَمَّدٍ Allahumma salli wa sallim ala Nabiyyina Muhammad. 🤍 JUMA’A MUBARAK! 📢 Ka yi salati ga Annabi ﷺ, ka kuma yaɗa wannan tunatarwa domin wasu su amfana.